You are here: HomeAfricaBBC2022 03 30Article 1502882

BBC Hausa of Wednesday, 30 March 2022

    

Source: BBC

'Yadda muka tsira daga harin 'yan bindiga a jirgin Abuja zuwa Kaduna'

Hoton yadda yan bindiga suka harbi jirgin kasa a hanyar Abuja zuwa Kaduna Hoton yadda yan bindiga suka harbi jirgin kasa a hanyar Abuja zuwa Kaduna

Fasinjojin da ke ke cikin jirgin kasan da 'yan bindiga suka kai wa hari a kan hanyarsu ta zuwa Kaduna daga Abuja sun bayyana yanayi irin na dimuwa da suka tsinci kansu a ciki.

Bayanai sun nuna cewa kimanin mutum 1000 ne a cikin jirgin, wanda aka kai wa hari ranar Litinin da daddare.

Rahotanni sun ce an sace mutane da dama sannan an kashe wasu, abin da ya jijjiga iyalai da 'yan uwan fasinjojin da ke cikin jirgin.

Daya daga cikin fasinjojin da ya sha da kyar ya shaida wa BBC yanayi na ukuba da suka tsinci kansu da yanayi na rudani da tashin hankali a lokaci guda.

Babu dai wasu cikakkun bayanai kawo yanzu kan yawan fasinjoji da suka rasa rayukansu ko adadin wadanda suka jikkata.

Sai dai wasu bayanan daga fasinjoji na cewa an ga gawawwaki da dama sannan mutane da dama sun jikkata daga harbe-harben bindiga.

'Harin ya fi shafar mata'

Usaman Mu'azu Saleh da ke kan jirgin ya shaida wa BBC cewa suna cikin tafiya kawai suka ji karar abu kamar bam ya tashi ya kuma girgiza jirgin, hakan na faruwa ba jimawa aka soma harbe-harbe.

Ya ce ya ga gawawwaki da dama, kuma abin ya fi shafar mata, saboda shi kansa a kan idonunsa ya ga gawawwakin mata uku zuwa hudu da aka harba.

"An kwashe fasinjoji da dama sun soma harin ne daga taragon baya, sai suka rinka bi tarago-tarago suna kwashe mutane da kashe na kashewa.

"Tun da misalin karfe 8 na saura na dare abin ya faru ake ta musayar wuta har zuwa wajen 9 da rabi".

Fasinja ya ce an shafe sama da awa guda 'yan bindigar na cin karensu babu babbaka kafin jami'an tsaro su zo kawo musu dauki.

Hakazalika shi ma wani Fasinja Sani Ibrahim da ya kubuta da kyar ya ce 'yan bindigar na bin kowane tarago suna haska mutane domin tantace na dauka.

Ya ce kusan babu taragon da basu shiga ba, da harbin mutanen da suka yi kokarin lalubo wayarsu da wani nau'i na abin haska wuri.

"'Yan bindigar suna da yawa ba zan iya tantace yawansu ba, amma har matar da ke zaune kusa da ni sun kashe ta.

"Sun umarci kowa ya kwanta a kasa, kar a motsa haka wasu daga cikinmu suka rinka dabbara jan jiki a jirgin domin shiga tarago na gaba.

"Sun yiwa jirgin kawayan saboda sun zo da motarsu da suka rinka kwashe mutanen domin garkuwa da su, sun soma ne da taragon farko wanda su ne manyan kujeru."

Malam Sani ya ce da safiyar yau Talata ya samu komawa gida, amma ya shaidi yadda fasinjoji da dama suka shiga yanayi na galabaita ga jini ta ko ina.

Ya kuma ce yana iya tuna ganin gawawwaki kusan goma da suka hada da mata da maza.

Sannan akwai bayanan da ke tabbatar da cewa harin ya shafi har wasu daga cikin fitattun mutane a kasar ciki harda tsohon gwamnan Zamfara Ibrahim Wakala wanda aka harba a cikin jirgin amma yana jinya a asibiti.

Tattara bayanan fasinjoji

Kusan fasinjoji dubu ɗaya ne ke cikin jirgin lokacin da aka kai musu harin.

Yanzu haka akwai mutane da dama da ke kwance a asibiti, sannan ana kan tattara bayanan fasinjoji domin tantace ainihin wadanda suka mutu da jikkata da kuma sanin adadin da aka sace.

Mutane da dama sun rugumi bin jiragen kasa saboda karuwar hare-haren da sace mutane a babban titin da ya hada Abuja zuwa Kaduna.

Kuma wannan shi ne karo na biyu da ake kai wa jirgin hari a cikin watanni shida.

Sace mutane domin neman kudin fansa ya kasance ruwan dare a arewacin Najeriya, kuma 'yan fashin daji kamar yada ake kiransu na sake karfi a muggan ayyukan da suke aikatawa.

Read full article