BBC Hausa of Tuesday, 25 April 2023
Source: BBC
Makonnin da suka gabata, Hiskandar Zulkarnaen ya je filin jirgin sama na Changi da ke Singapore, tare da matarsa da yaransa biyu a mota.
Kantin zamani na Jewel da ke da tsayin kafa mita 1.5 wanda ke kusa da inda fasinjoji ke zama domin jiran jirgi nan za su je, wani kwararran mai zane ɗan kasar Canada ne Moshe Safdie da tawagarsa suka zana kantin.
Yaransa na son zuwa hawa na bakwai saman inda suwa ke juyawa, wani gini mafi tsayi da ake a duniya da aka yi inda ruwa yake gangarowa, ga kuma fitilu da kiɗa da yake tashi.
Iyalan nasa sun tsaya a wurin da ake jiran jirgi na uku ‘yan mintina gabanin su ɗauki mota ko jirgin ƙasa mai amfani da wuta, yana yi wa yara daɗi saboda suna buga wasan intanet a ciki.
“Na ƙara samun wayewa game da wani filin jirgin sama da aka yi domin jin daɗi, hutu da kuma zama domin cin abincin dare,” in ji Zulkarnaen, wanda ya nuna sha’awar zuwa Changi da ziyarar titin Orchard, wani kantin zamanin Singapore mafi shahara a duniya.
Barka da zuwa filin jirgi mafi kyau a duniya kamar yadda Skytrax ta bayyana, wata tawagar jami’ai kwararru da take bayyana filayen jirgin da suka fi ko waɗanne a duniya.
Kamfanin Skytrax ta yi wani bincike na shekara kan yadda abokan hulɗa ke gamsuwa da kulawar da ake ba su a filayen jiragen sama, inda matafiya ke samun kulawa da amfani da kayayyakin aiki a fiyalen jirgi sama da 550.
Filin jirgin Changi shi ne na ɗaya kashi na 12 a jerin bayanan kamfanin Skytrax, ciki har da na ɗaya da yazo sau takwas a jere cikin shekara 10 da suka gabata.
Ya koma na ɗaya ne a watan Maris, bayan filin jirgin sama na Hamad da ke Doha da na Haneda da ke Tokyo sun yi n ɗaya a shekara biyu da suka wuce, waɗanda suka samu nasara bayan bayanan da abokan hulɗarsu suka bayar a kansu.
Gabanin annobar korona a 2019, jirage 382,000 ne ke ta shi ko sauka a filin Changi, sun ɗauki fasinjoji sama da miliyan 68. Yayin da yake ci gaba da riƙe ƙimarsa a idon fasinjoji, Changi ba kawai ana son hi ba ne a matsayin filin jirgin yin tafiya, a a akan zuwa wajen domin shaƙatawa, a wajen masoya a Singapore.
Yana da sauƙin zuwa a mota ko jiragen kasa na cikin gari, ba wani abun mamaki ba ne yadda mutane ke share yini guda a bakin wajen suna hutawa. Za aka iya kallon fim da cin abinci za ka iya zama ka yi karatun jarrabawa a ƙofar filin jirgin saman.
Cikin shekaru mutane na amfani da wurin a matsayin wajen ɗaukar hotunan aure da kuma haɗuwar abokai.
Cikin abubuwan da ke jan hankai a wurin akwai wani yanayin sanyi kamar na cikin daji, da wata ƙatuwar masara da aka ƙera da kuma wajen wasan sululu mai tsayin mita 12.
Idan tafiya ta kamaka ka isa filin da wuri akwai wuraren tausa da kallon fim da wajen wanka kyauta, ba a maganar kujerar da ke yi wa mutum tausa da kuma wani lambu mai cike da malam buɗa mana littafi.
Filin yana da wani ƙamshi da yake yi na daban: wanda ya samu asali daga wasu turaruka da wasu nau’ukan na daban.
A wajen ginin wurin da ake jiran jirgi na hudu, akwai katon hoton wani jegare a jikin majigi.
Duk da cewa wasu wurare sun rufe lokacin annobar korona, gwamnati ta yi alƙawari sake farfado da darajar filin, ta yadda ta sanya biliyoyin dalar Singapore a bangaren sufurin jiragen sama.
Ministan sufuri na Singapore ya ce an yi hakan ne domin dawo da ƙimar filin a idon duniya ta fuskar kasuwanci.
“In ba Chnagi ba ne na ɗaya to yana cikin manyan filayen jiragen sama na duniya,” in ji Alex Chan da ke zaune a zurich, wanda ya shiga filin sau huɗu a tafiye-tafiyensa.
Duk da ‘yar matsalar da aka samu a wajen na’urar da jami’an lura da shige da fice suke aiki da ita domin tantance matafiya, da yawan matafiyan sun zaɓe ya da zango a Changi a mwatayin wata damar kwallacewa idanunsu abubuwan kallo, in ji Shukor.
“Ka dubi lokaci da kuɗi da makamashi da ake sanyawa a filayen jirage, zaka ga na Singapore ya yi wa kowanne nisa,” in ji shi.
Idan aka yi waiwaye a shekarun 1990, lokacin da ba wani abun kallo a Singapore sai wani wasan kwaikwayo da ake haskawa a gidan talabijin na ƙasar, amma yanzu Changi ya zama wani gagarumin abin kallo a ƙasar.
A 2019, Jewel ya karɓi baƙi miliyan 50 a wata shidan farko da aka buɗe shi. Yanzu ana gina wurin jiran jirgi na biyar kuma ana sa ran zai fara aiki a 20230.
“Bana tsammanin akwai wani filin jirgin sama da zai faɗaɗa karɓar baƙi daga cikin gida,” in ji Adrian Tan, wani lauya mai sharhi kan lamuran yau da kullum.
“Shi yasa Changi ya zama na daban. Yana nuna irin kyan da Singapore ke da shi: girma da kuma mutuntawa shi ne burin ‘yan Singapore.”