BBC Hausa of Monday, 27 March 2023
Source: BBC
Hukumar lura da yanayi ta Najeriya NiMet ta yi gargaɗin cewa za a fuskanci tsananin zafi a wasu jihohin Najeriya.
A wata sanarwa da ta fitar ranar Lahadi, NiMet ta ce yanayin wanda ake sa ran ya fara daga Litinin zai iya haura digiri 40 a ma'aunin salshiyas.
Jihohin da aka yi hasashen za su fuskanci ƙaruwar yanayi na zafin rana sun haɗa da Kebbi da Sokoto da Zamfara da Taraba da Adamawa da Oyo da Kwara.
Sai kuma birnin Tarayya Abuja da Nasarawa da Benue da Bauchi da Gombe da kuma Borno.
Nimet ta ce za a fuskanci yanayin na zafin rana ne a tsawon kwanaki biyu masu zuwa.
Nimet ta ce jihohin da makin zai haura 40 sun haɗa da wasu sassan Sokoto da Kebbi da Zamfara da Taraba da kuma Adamawa.
Hukumar ta sharwarci mutane da ke zaune a jihohin da abin zai shafa, da su riƙa shan isasshen ruwa a tsawon lokacin.
Sai dai lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da al'umma musulmi ke gudanar da azumin Ramadana a Najeriyar da ma sauran ƙasashen duniya.
Hanyoyin kare kai