You are here: HomeAfricaBBC2023 05 23Article 1772408

BBC Hausa of Tuesday, 23 May 2023

    

Source: BBC

'Yan Barca da za su kara da Valladolid a La Liga

Robert Lewandowski Robert Lewandowski

Barcelona ta je gidan Real Valladolid, domin buga wasa na 36 a gasar La Liga ranar Talata.

Barcelona ta doke Valladolid 4-0 a wasan farko a kakar bana da suka kara ranar Asabar 28 ga watan Agustan 2022 a Camp Nou.

Robert Lewandowski ne ya ci biyu a wasan, sauran da suka zura kwallayen a raga sun hada da Pedri da Sergi Roberto.

Tuni Barcelona ta lashe kofin La Liga na bana na farko tun bayan 2018/19 kuma na 27 jimilla.

Barcelona tana matakin farko da maki 85, ita kuwa Valladolid mai maki 35 tana ta 18 a kasan teburin La Liga na kakar nan.

Tuni Xabi ya bayyana 'yan wasan da ya je da su Valladolid, domin buga fafatawar.

'Yan kwallon Barcelona:

Ter Stegen, Sergio, O. Dembélé, Lewandowski, Ansu Fati, Ferran, Iñaki Peña, Christensen, Marcos A., Jordi Alba, Kessie da kuma S. Roberto.

Sauran sun hada da F. De Jong, Raphinha, Eric, Balde, M. Casadó, Gavi, Pablo Torre da kuma Arnau Tenas.

Mai tsaron baya, Jules Kounde ba zai buga karawar ba, wanda har yanzu ke jinya.

Wasannin da za a buga ranar Talata 23 ga watan Mayu:

  • Celta Vigo da Girona


  • Real Sociedad da Almeria


  • Real Valladolid da Barcelona


  • Read full article