BBC Hausa of Wednesday, 21 June 2023
Source: BBC
Da alama dai ‘yan Najeirya na iya fuskanatar ƙarin kuɗin wutar lantarki fiye da kashi arba’in cikin dari nan da wasu kwanaki, idan har sabuwar dokar wutar lantarki ta fara aiki.
Ana sa ran cewar dokatar za ta bai wa shugaban Najeriya damar janye tallafin kusan naira biliyan hamsin da gwamantin kasar ke kashewa a bangaren wutar lantarki a Najerya.
Ana sa ran masu ruwa da tsaki a fannin wutar za su yi wani zama da hukumar da ke kula da rarraba wutar lantarki a ranar daya ga watan Yuli don ɗaukar matsaya a kai.
Su dai masu ruwa da tsaki a bangaren na kallon hakan a matsayin wani cigaba, la'akari da yadda tsarin samar da wutar lantarki yake a sauran kasashen duniya.
Daya daga cikin 'yan kwamitin kula da harkar wutar lantarki a majalisar wakilan Najeriya da ta gabata Injiniya Sani Bala Tsanyawa, a wata hira da BBC ya ce ba shi da tabbacin yadda karin zai kasance sai dai a bisa yadda abubuwan suke musamman yadda kamfanonin wutar ke ta korafi, ba mamaki a kara kudin da kusan kashi 40 cikin dari.
Me dokar ta ce?
Dan majalisar wakilan ya ce dokar ta tanadi ba wa jihohi da dai-daikun jama'a damar samar da wutarsu, da kuma sarrafa ta da rarraba ta.
Ya ce manufar ita ce ba wa masu hannu da shuni damar shiga harkar, tun da ta bayyana cewa gwamnati ba za ta iya ba wa jama'ar kasar baki daya wuta ba.
''Akwai manyan masu kudi da kamfanoni da ke son su yi hakan, to amma babu doka, don haka wannan mataki a yanzu zai sa wutar ta wadata, sannan ya kasance an yi abun bisa tsari'' in ji shi.
Ya kara da cewa: ''Dama ita wuta a yanzu an riga an wuce zamanin samunta a kyauta, ba aba ce da samunta ke da sauki ko araha ba''.
Ana kukan targade...
A baya-bayan nan ne gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta kara farashin litar mai bayan janye tallafinsa da aka yi, lamarin da ya sa 'yan kasar da dama guna-guni.
Karin farashin muhimman abubuwa kamar man fetur da wutar lantarki a Najeriya na haifar da tashin farashin komai da ake amfani da shi, domin ko da aka kara kudin man fetur a baya-bayan nan an samu tashin farashin kusan komai da ninkin baninkin.
Har yanzu ana ci gaba da kai ruwa rana tsakanin 'yan kwadago da gwamnati kan mafi karancin albashi na Naira dubu dari biyu da 'yan kwadagon ke ganin an amince da shi sakamakon karin man da aka yi.
Sai kuma ga wannan batu na karin kudin wuta da ya taso a yanzu.