BBC Hausa of Wednesday, 19 April 2023
Source: BBC
Wata ƙididdiga daga Majalisar Ɗinkin Duniya ta nuna cewa a tsakiyar bana ne, Indiya za ta zarce China a matsayin ƙasa mafi yawan al'umma a duniya.
Ana sa ran yawan jama'ar Indiya zai kai mutum biliyan 1.4286 - zai fi yawan maƙwabciyarta da miliyan 2.9 wadda al'ummarta za su kai biliyan 1.4257.
Ƙasashen na nahiyar Asiya su ne ke da fiye da kashi ɗaya cikin uku na al'ummar duniya tsawon sama da shekara 70.
Alƙaluman haihuwa a China sun ragu sosai a baya-bayan nan, inda yawan al'ummarta ya ragu ja baya karon farko tun a 1961.
Hasashen da aka yi kan yawan al'ummar Indiya cikin rahoton Hukumar kula da yawan al'umma ta Majalisar Dinkin Duniya UNFPA, ƙiyasi ne tun da ba a yi ƙidayar jama'a ba a ƙasar tun shekara ta 2011.
Sannan Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce ƙididdigar ba ta haɗa da yawan al'ummar yankin Hong Kong da Macau ba - ko tsibirin Taiwan da China ke kallo a matsayin lardin da ya ɓalle kuma wata rana zai haɗe da babban yankin ƙasar.
Taiwan na kallon kanta daban daga China, inda take da tsarin mulki da kuma shugabannin da aka zaɓa bisa tafarkin dimokraɗiyya.
A watan Nuwamba, yawan al'ummar duniya ya kai biliyan 8.
Amma ƙwararru sun ce ƙaruwar jama'ar ba ta kai yadda take a baya ba, kuma a yanzu tana tafiyar hawainiya tun cikin 1950.
China da Indiya sun fuskanci koma-baya a alƙaluman yawan haihuwa.
Hakan na nufin a China, yawan jama'arta zai fara raguwa a shekara mai zuwa duk da yake ƙasar ta yi watsi da tsarin nan na haihuwa sau ɗaya a shekara ta 2016.
Ta kuma bijiro da wasu hanyoyi na jan hankalin ma'aurata su haifi yara biyu ko fiye da haka.
Tsadar rayuwa da ƙaruwar matan da ke aiki na cikin abubuwan da ake ganin suna yin tasiri wajen rage yawan al'ummar China.
A Indiya ma, yawan haihuwa ya ragu a shekarun baya-bayan nan daga haihuwa 5.7 ga kowacce mace a 1950, zuwa haihuwa 2.2 ga duk mace a yanzu.
A wani nazari da UNFPA ta yi, akasarin ƴan Indiya sun ce yawan jama'ar ƙasar ya tumbatsa, kuma alƙaluman haihuwa ya ƙaru.
Kusan mutum biyu cikin uku na mutanen sun bayyana batun tattalin arziƙi a matsayin babban abin damuwa, idan ana magana kan ƙaruwar al'umma.
Masu nazari sun ce bai kamata a nuna damuwa idan yawan al'ummar Indiya ya wuce na China ba.
"A maimakon haka, kamata ya yi a kalli lamarin ta fuskar ci gaba da kuma fatan idan aka tabbatar da haƙƙoƙin jama'a da zaɓinsu," in ji rahoton na Majalisar Ɗinkin Duniyar.