BBC Hausa of Thursday, 8 June 2023
Source: BBC
Gwamnatin Kenya ta ce ta tattara isassun hujjojin gurfanar da faston nan Paul Mackenzie bisa zargin yin kisan kiyashi.
Mr Mackenzie ya yi wa mabiyansa fatawar cewa duniya ta zo ƙarshe, sannan ya buƙace su da su yi azumin da zai zamo silar mutuwarsu ta yadda za su haɗu da Yesu.
Ya zuwa yanzu an gano gawarwaki 250 na mabiyansa, waɗanda aka tono a ƙaburbura da ke a wani daji na ƙasar.
Kuma har yanzu ana ci gaba da neman mutune 613 waɗanda ba a san inda suke ba.
Har yanzu dai ana ci gaba da jimamin lamarin, inda a ranar Talata aka ƙara gano gawarwaki tara daga dajin na Shakahola.
Paul Mackenzie ya ayyana dajin Shakahola a matsayin wuri mai tsarki.
Yanzu ana tuhumarsa da sanya mabiyansa su yi azumi wanda ya yi sanadiyyar mutuwarsu, bisa hujjar cewa duniya ta zo ƙarshe.
Minsitan harkokin cikin gida na Kenya, Kithure Kindiki ya ce yanzu masu bincike sun tattara isassun hujjoji masu ƙarfi da za a gurfanar da faston da muƙarrabansa.
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na twitter, ministan ya ce za a gurfanar da su kan laifukan da suka shafi kisan kiyashi.
Ya shaida wa manema labaru cewa za su yi amfani da dokoki na ƙasa da ƙasa wajen tuhumar faston.
Ya kuma tabbatar da cewa yanzu an faɗaɗa neman gawarwaki zuwa wasu wuraren baya ga dajin Shakahola - wanda a yanzu za a ayyana shi a matsayin wajen alhini na ƙasa.