You are here: HomeAfricaBBC2022 06 09Article 1556945

BBC Hausa of Thursday, 9 June 2022

    

Source: BBC

Za mu hana masu karancin shekaru mallakar bindiga - Nancy Pelosi

Wasu da suka rasa iyalai saboda harbi da bindiga Wasu da suka rasa iyalai saboda harbi da bindiga

Majalisar Wakilan Amurka ta amince da wasu sababbin matakai domin magance matsalar rasa rayuka da ake yi daga harbi da bindiga - ciki har da kara yawan shekarun wanda ka iya sayen baindiga mai sarrafa kanta.

Sai dai ana bukatar 'yan majalisa akalla 60 kafin kudurin ya sami amincewar majalisar dattawan kasar

Idan ba a sami 'yan majalisa sittin a majalisar dattawa ba, kudurin ba zai yi tasiri ba, kuma da alama rarrabuwar kawuna a siyasance zai tabbatar da haka lamarin zai kasance.

Kakakin majalisar wakilai Nancy Pelosi ce ta sanar da sakamakon kuri'ar da aka kada:

"A kan wannan batu, wadanda suka amince mutum 223 ne, inda wadanda ba su amince ba kuma mutum 204 ne. Wannan na nufin an amince da kudurin ke nan."

Sai dai sanatoci daga dukkan jam'iyyun siyasa biyu na Amurka na duba wani kudurin da bai kai na majalisar wakilan tsauri ba.

Shi wannan matakin ya biyo bayan jerin harbe-harben da aka yi a kasar ne, ciki har da wanda aka yi a wata makaranta da ke jihar Texas, wanda wani matashi dauke da bindiga mai sarrafa kanta ya yi sanadin mutuwar dalibai 19 da malamansu biyu.

Read full article