You are here: HomeAfricaBBC2022 04 01Article 1504892

BBC Hausa of Friday, 1 April 2022

    

Source: BBC

Ƴan bindiga sun fi gwamnatin Najeriya hanyoyin samun sahihan bayanan sirri - Bukarti

Yan bindiga sun addabe yan Najeriya musamman arewacin kasa Yan bindiga sun addabe yan Najeriya musamman arewacin kasa

Hanyoyin tattara bayanan ƴan bindigar da suka addabi arewa maso yamma da arewa ta tsakiyar Najeriya sun fi na gwamnati sahihanci a halin da ake ciki a yanzu kan lamarin tsaron ƙasar, a cewar Barista Audu Bulama Bukarti, mai bincike kan tsaro a yankin Saleh a Cibiyar Tony Blair da ke Birtaniya.

Ya shaida wa BBC Hausa hakan ne a ranar Alhamis a daidai lokacin da masu sharhi a ƙasar suka fara tofa albarkacin bakinsu a kan kalaman da aka jiyo ministan sufuri na Najeriya Rotimi Ameachi ya yi.

An jiyo Ameachin na bayyana takaici a kan gazawar hukumomi wajen sanya na'urar tsaron zamani da za ta iya kare layin dogo daga hari irin wanda aka kai kan jirgin ƙasa ranar Litinin.

Kalaman ministan sun jawo ce-ce-ku-ce sosai a ƙasar da kuma saka wasi-wasi a zuƙatan mutane.

Barista Bukarti ya ce ya fahimci manyan abubuwa biyu ne daga kalaman ministan da suka haɗa da alamar da ke nuna ɓaraka a cikin gwamnatin Buhari da kuma nuna miƙa wuyan muƙarraban gwamnatin na cewa abin ya wuce tunaninsu.

"Abu na farko da kalaman ministan ke nunawa shi ne cewa an fara samun ɓaraka a gwamnatin, domin kuwa a da ba za ka taɓa jin minista, kai ko mai ba da shawara, ko mai bin bayan gwamnati ma ba zai fito ya yi irin waɗannan maganganu da ya yi ba.

"Abu na biyu, ina ga dalilin abin da ya sa wannan abu ya faru na fusatar minsitan da kuma maganganun da ya yi shi ne, cewa hatta jami'an gwamnatin yanzu sun fahimci cewa ba sa nasara a yaƙin nan, ga shi kuma sukuwa ta ƙare saura zamiya," in ji mai sharhin.

Mai bincike kan tsaron ya ce a yanzu gwamnatin ba ta da isasshen lokacin da za ta gyara kura-kuran da ta yi.

Sannan ya ce maganganun da ministan ya yi suna da matuƙar amfani domin kuwa a duniyar yau, ba yaƙi ake na fi da ƙarfi ba, yaƙi ne ake na dabara, kuma wannan dabara ana amfani da fasahar zamani ne.

Amfani da fasaha don kare hari a jirgin ƙasa

Amma tambayar da za ta fi zuwa zuƙatan mutane ita ce ta yaya za a yi amfani da fasaha wajen hana kai hari a kan jirgin kasa?

Barista Bukarti ya ce yadda za a yi amfani da fasahar da farko shi ne tattara sahihan bayanai.

"Domin da da akawai fasahar da ministan yake fada babu yadda za a yi wani ya zo ya ɗora bam a kan layin dogon jirgin ba tare da an hango shi tun daga garin Abuja ba.

"Kuma da an hango su, na farko za a iya dakatar da su daga abin da suka shirya. Abu na biyu kuma za a iya dakatar da jirgin daga tahowa.

"Wato dai misali ne na fasahar da jiragen sama ke amfani da ita su hango hatta guguwa daga nesa su fasa tashi ko kuma su fasa tafiya su koma ko su fara sauka," a cewar Bukarti.

Wasu na cewa akwai al'amura da dama da ba a fahimce su ba a yaƙi da masu ta da ƙayar baya, ko harin baya-bayan nan na nuna akwai sauran jan aiki, ko yaya mai binciken ke ganin wannan batu?

Ya ce: "Ƙwarai da gaske, wannan harin na nuna cewa akwai babban jan aiki a gaban gwamnati, kuma rashin isassun sahihan bayanai ne a kan yanayin da ake ciki.

"Sannan da kuma azarbaɓin wadansu da ke gwamnatin masu kokarin su yi tafi su ce sun yi nasara a daidai lokacin da ba su yi nasara ba."

Ya ce masu sharhi irinsa sun ɗauki lokaci a kalla shekara biyu suna gargaɗi tare da jan kunnen gwamnati cewa akwai ɓata gari masu matukar hatsari da suka yaɗu a yankin arewa ta tsakiya da arewa maso yamma.

"Gwamnatin kuma ta zo tana karyata abin da muke faɗa a kakafen yada labarai irin BBC, daga baya ta zo ta fara yarda amma kuma ba a dau matakan da suka dace ba," a cewar Bukarti.

"Ba a makara ba"

Sai dai mai binciken na ganin ba a yi latti ba, har yanzu za a iya daukar isassun matakai.

Ya ce na farko a yi amfani da fasaha, domin a yanzu maganar da ake, hanyoyin tattara bayanan ƴan bindigar nan ya fi na gwamnati sahihanci.

Sannan ya ƙara da cewa akwai mutanen da suke amfani da su a cikin al'umma wadanda su ma mambobinsu ne.

"Idan an kula wadansu da ke cikin jirgin da aka kai wa hari suna magana, su 'yan bindigar sun ma san taragon da mutanen da suka fi maiƙo ke ciki.

"Nan suka fara kai hari kuma suka ce lallai sai sun fasa shi, har ma in sun kama mutum sai sun tambaya ko shi ne dan majalisa kaza da kaza," ya ce.

Barista Bukarti ya kammala da cewa wannan na nuna ƙarfin tattara bayanan da suke yi, kuma suna iya zuwa har su saka bam a kan titin layin dogo, su kuma taru su yi kwanton ɓauna amma ita gwamnati ba ta iya tattara bayanai ta gane cewa suna wannan kisisinar ba.


Read full article