You are here: HomeAfricaBBC2023 07 31Article 1815815

BBC Hausa of Monday, 31 July 2023

    

Source: BBC

Ɗan kunar bakin wake ya kashe kusan mutum 50 a Pakistan

Hoton alama Hoton alama

Wani dan kunar bakin wake a Pakistan ya tayar da bama-baman a wani gangamin siyasa a arewa maso yammacin Pakistan.

Jami'an tsaro sun ce lamarin ya kashe mutum 44, kana sama da 200 sun jikkata a gangamin siyasar jami'iyyar JUI-F, a gundumar Bajour.

A wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan lardin ta fitar ta ce dan kunar bakin waken ya tayar da bama-baman da ke jikinsa ne a kusa da dandalin da wasu manyan shugabannin jam’iyyar ke zaune.

Sanarwar ta ce binciken farko ya nuna cewa da alamun kungiyar ISIS ta Pakistan ce ke da hannu a lamarin.

Kungiyar da ke dauke da makamai ta yi ta kai hare-hare a makwabciyar Pakistan wato Afghanistan bayan hambarar da gwamnatin shugaba Ashraf Ghani, inda take adawa da gwamnatin Taliban ta Afganistan din, kuma tana da mambobinta da suka tsalaka tsaunuka suka shiga Pakistan, suka buya a Peshawar.

Kakakin jam'iyyar ta JUI-F, Jalil Jan, ya yi kira da a gudanar da bincike kan tashin bama-baman:

"Idan babu zaman lafiya a kasar nan, babu wanda zai saka hannun jari a nan don kasuwanci, don haka muna bukatar zaman lafiya a Bajaur, gundumar Mohmand da kewaye, muna Allah wadai da wannan tashin boma bomai, muna neman a gudanar da bincike kan wannan lamarin don gano wanda ke da hannu a cikinsa'' inji shi.

Yanzu haka dai an ayyana dokar ta-baci a Bajaur da kuma yankunan da ke makwabtaka da inda aka kai harin.

An kwashe wadanda suka jikkata daga Bajaur zuwa asibitoci a Peshawar da jirage masu saukar ungulu na sojoji.

Firaminista Shehbaz Sharif ya yi Allah wadai da harin da kakkausar murya, tare da mika ta'aziyyarsa ga iyalan wadanda abin ya rutsa da su, ciki har da na shugaban jam’iyyar ta JUI-F Ziaullah Jan, wanda aka tabbatar da kashe shi a harin.

Read full article