You are here: HomeAfricaBBC2023 07 13Article 1803917

BBC Hausa of Thursday, 13 July 2023

    

Source: BBC

Ƙasashen Afirka biyar da ke gab da kawar da cutar HIV

Hoton alama Hoton alama

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya ce duniya na kan hanyar kawar da cuta mai karya garkuwar jiki wato HIV/AIDS zuwa shekara ta 2030 matukar aka zuba kuɗi a ɓangaren lafiya da ke da muhimmanci.

A kasashen yankin Kudu da hamadar Saharar Afirka ne ake da kashi 65 cikin 100 na masu ɗauke da cutar HIV, kuma suna kokari wajen ganin an kawar da cutar daga yankin.

Tuni kasashen Bostwana da Eswatini da Rwanda da Tanzania da kuma Zimbabwe suka cimma kudurin kawar da cutar da kashi 95 cikin 100, in ji Majalisar Dinkin Duniya.

Wannan na nufin kashi 95 cikin 100 na mutanen da ke dauke da cutar sun san matsayinsu sannan kuma suna karbar magani, kuma na samun sauki, kuma da wuya su yada cutar.

Akwai wasu kasashe 16, takwas daga cikinsu a yankin Kudu da hamadar Saharar Afirka wadanda suka kusa cimma wannan muradin.

Babbar daraktar sashen yaki da cutar HIV a Majalisar Dinkin Duniyar, Winnie Byanyima, cikin wata sanarwa ta ce, " Kawo ƙarshen cutar Aids wani babban abin alfahari ne na musamman ga shugabannin Afirka na yanzu."

Ta ci gaba da cewa, " Za su iya kare miliyoyin rayuka, sannan su nuna abin da ya kamata shugaba ya yi ke nan."

To amma, sashen da ke kula da masu cutar HIV din a Majalisar Dinkin Duniya na fama da karancin kudin da ya kai dala biliyan takwas da miliyan dubu dari biyar na kudaden da take son amfani da su wajen kawar da cutar zuwa nan da shekara ta 2025.

Ta ce za a samu ci gaba wajen kare mutane daga kamuwa da cutar idan aka yi abin da ya dace.

Yara mata na cikin hatsari

To amma akwai wasu abubuwa da suka dakile cimma wannan buri. A kowanne mako, ana samun yara mata matasa da kuma kananan matan da ke kamuwa da cutar HIV.

A kasashen yankin Kudu da Saharar Afirka, duk da ci gaban da ake samu wajen kawar da cutar, akwai kashi 63 cikin 100 na yammata da kananan matan da ke kamuwa da cutar.

A Bostwana da ke Kudancin Afirka, yammata na fuskantar cin zarafi inda manyan maza ke lalata da su a wani abu da aka sani da cewa lalata tsakanin tsoho da yarinya.

Gaone, shekarunta 32, ta kuma kamu da cutar HIV tun ta na makaranta.

Ta ce, " Daya daga cikin 'yan uwana na kusa da ya saba taimaka mini sosai wanda kuma shekarunsa suka kai talatin da wani abu a lokacin ma'ana ya rubanya shekaru a lokacin, na amince da shi sosai sai ya yi amfani da wannan damar ya yi lalata da ni."

Gaone, ta kasance tana shan maganin cutar HIV tun 2012, tana kuma da 'ya'ya biyu.Yaran nata ba su da cutar, kuma a yanzu ta zamo daya daga cikin masu gangamin yaki da wannan cuta.

Ta ce har yanzu mutanen garuruwansu ba su shirya yin tattauna a fili a kan matsalar fyade da cin zarafi ta hanyar lalata ba.

Ta ce, " A yawancin lokuta iana samun sakonnin mata akalla biyar da suka kamu da cutar HIV daga manyan maza, kuma yawanci 'yan uwansu.Idan har maza ba sa jin magana to mu ya zamu yi ke nan?"

The power of prayer

Kididdiga ta nuna cewa mazan da suka kamu da cutar HIV sun fi jan kafa wajen neman magani fiye da mata.

A yanzu Bostwana na sanya malamin addini wajen kokarin sauya wannan hali na maza don kare yaduwar cutar.

Rebaran Mmachakga Mpho Moruakgomo, ya ce " A Bostwana kashi 95 cikin 100 na mutanen da ke dauke da cutar HIV sun san matsayinsu, wadanda ba su sani ba maza ne."

Ya ce, " Tun da mutane na girmama shugabannin addininsu, muna amfani da damar wajen tattauna da maza a kan bukatar da ke akwai ta yin gwaji da fara karbar magani idan har aka tabbatar da mutum na dauke da cutar."

Rev Moruakgomo, ya ce " Shugabannin addinin Musulunci da Hindu da kuma na Bahai da ma masu maganin gargajiya duk suna irin wannan wayar da kai da muke, wasu ma a cikinmu har gida-gida suke bi don isar da wannan sako."

Wani malamin addinin kirista ya ce, " Akwai tsangwama sosai a kan masu dauke da cutar HIV. Mu shugabannin addinin mu ne alhakin kawar da hakan ya rataya a kanmu."

Ya ce, " A kodayaushe muna yake hukuncin cewa yawanci wadanda ke lalata ne ke kamuwa da cutar, yakamata mu sani saduwa tsakanin mata da maza wani abu ne da ya zama doke musamman ga ma'aurata, to amma yakamata mu sani saduwa tsakanin wadanda ba ma'aurata ba ita ce marar kyau, kuma a irin saduwa ne idan aka kamu da wannan cuta za a kyamaci mutum, to idan har mijin mace ne ya sanya mata fa, ya za ayi ke nan? yakamata mu gyara tunaninmu."

To amma duk da wannan kalubale da ake fuskanta, akwai ci gaba sosai wajen kawar da cutar HIV a Bostwana in ji jami'in lafiya a kasar Ontiretse Letlhare.

Halin da sauran kasashen duniya ke ciki wajen yaki da cutar HIV

Majalisar Dinkin Duniya ta ce kusan kashi daya bisa uku akeasamun mutanen da suka kamuwa da cutar HIV a kasashen Asiya da Pacific a 2022.

To amma a kasashen nahiyar Turai ana samun karuwar wadanda ke kamuwa da cutar musamman a yankin gabashin Turai da tsakiyar Asiya inda aka samu karuwar da kashi 49 cikin 100 tun 2010. A kasashen gabas ta tsakiya da arewacin Afirka kuwa an samu katruwar masu da cutar da kashi 61 cikin 100 tun 2010.

Majalisar ta ce an samu wannan karuwa ce saboda rashin amfani da abubuwan kariya da kuma batun dokokin uaren jinsi da ake da su a wasu kasashen.

Cambodia da ke gabashin Asiya, na samar da wani magani kyauta ga mutanen kasar musamman ga masu auren jinsi da makamantansu.

Kwayar wadda ake shanta a kullum, na dauke magungunan da masu cutar HIV ke amfani da su kuma tana aiki sosai don ta na ma kare mutum daga kamuwa da cutar.

Ta ce, " Sai da na sha kwayar da tsawon watanni uku.Da farko na rinka fuskantar ciwon kai daga baya kuma sai na daina jin komai.Ina shan kwara saboda ni mata maza ce.

Ta ce, " Ina sha kwayar ta PrEP, ne saboda ina saduwa da mutane kala kala, na san ina cikin hadari kuma yawanci na kan cewa abokan badalata su sanya kwaroron roba kamu mu sadu, to amma su kan ki a wani lokaci."

A Cambodia, an kiyasta cewa akwai mutum dubu 76 da ke dauke da cutar HIV.Kuma yawancinsu sun san matsayinsu sannan sun shan magani.

A yanzu an samu raguwar masu kamuwa da cutar sosai idan aka kwatantan da 1996.Saboda ana samun mutum hudu da ke kamuwa da ita ne a kowacce rana abin har yanzu akwai damuwa.

Ya ce, " A baya an rinka wayar da mutane a kan amfani da kwaroron roba, to amma yawanci wasu basa yi. Kwayar PrEP, wata sabuwar hanya ce don taimakawa mutane kare kansu daga kamuwa da cutar HIV da ma yada ta."

Kwayar PrEP, na taimakawa sosai kuma yanzu ana duba yadda za a samar da allurarta in ji Danou Chy.

Wannan sabuwar dabara ta taimakawa Kuy a rayuwarta.

Ko a baya bayan nan ta yi gwajin cutar kuma an tabbatar da cewa bata dauke da ita.

Read full article