You are here: HomeAfricaBBC2023 07 30Article 1814753

BBC Hausa of Sunday, 30 July 2023

    

Source: BBC

Ƙasashen Yamma masu dakarun sojoji a Nijar

Hoton alama Hoton alama

Nijar, babbar abokiyar ƙawance ga Ƙasashen Yamma a yaƙin da suke yi da 'yan ta-da-ƙayar-baya masu iƙirarin jihadi a yankin Sahel na Afirka ta Yamma, tana karɓar baƙuncin wani adadi na dakarun sojin ƙasashen waje.

Adadin waɗannan sojoji ya ƙaru a cikin shekara biyu da ta wuce bayan juyin mulkin sojoji a Mali da Burkina Faso, wanda ya sa dangantaka ta yi tsami tsakaninsu da abokan ƙawancensu na Yamma.

Hamɓaras da Shugaba Mohamed Bazoum da sojoji suka yi, lamari ne da ke barazanar sanya tsamin alaƙa tsakanin Nijar da Ƙasashen Yamma.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya tattara bayanai a kan Ƙasashen Yamma da ke da dakarun sojoji a Nijar. Ga su kamar haka;

Faransa

Faransa, tsohuwar uwargijiyar da ta yi wa Nijar mulkin mallaka tana da dakarun soji tsakanin 1,000 zuwa 1,500 a ƙasar, inda suke samun taimakon kayan aiki kamar jirage marasa matuƙa da sauran jiragen yaƙi masu matuƙa. Tana da dakarun murƙushe 'yan ta-da-ƙayar-baya a Afirka ta Yamma tsawon shekara goma, sai dai ta koma Nijar don girke dumbin dakarunta a sansani bayan jerin juyin mulki a maƙwabtan ƙasashe kamar Mali a 2021 da kuma a Burkina Faso a 2022.

Faransa dai ta ce matsayin dakarunta shi ne kawai su taimaka wa sojojin Nijar a duk lokacin da dakarun ƙasar suka shaida wasu ayyuka a yankunan kan iyaka masu alaƙa da Mali da kuma Burkina Faso.

Hukumomin birnin Paris na neman kaucewa yiwuwar fuskantar suka kan matsayinta a Sahel da kuma rage kaifin ƙin jinin Faransa ta hanyar mayar da hankalinta wajen tallafawa dakarun cikin gida, maimakon ganin sojojin Yamma a cikin ayyukan tsaro a ƙasa.

Amurka

Akwai kimanin dakarun Amurka 1,100 a Nijar, inda sojojin Amurka ke gudanar da harkokinsu daga wasu sansanoni guda biyu. a 2017, gwamnatin Nijar ta amince wa Amurka da amfani da jirage marasa matuƙa don kai hari a kan mayaƙa 'yan ta-da-ƙayar-baya.

Babu bayani ƙarara na ko nawa Amurka ta bai wa Nijar a matsayin tallafi kan harkokin tsaro. Ofishin jakadancin Amurka a birnin Niamey a 2021 ya ce ma'aikatar tsaro ta Pentagon da ma'aikatar harkokin wajen Amurka sun samar wa Nijar kayan aiki da horon sojoji da suka zarce na dala miliyan 500 tun a shekara ta 2012.

Italiya

Italiya na da sojoji kimanin 300 a Nijar, a cewar ma'aikatar tsaron ƙasar.

Tarayyar Turai

Ƙungiyar ƙasashen tana da dakarun soja 50 zuwa 100 don wani aikin horar da sojoji na tsawon shekara uku. Ta kafa shirin a Nijar ne a cikin watan Disamba don taimaka wa ƙasar wajen inganta harkokin sufurin sojoji da samar da kayan aiki.

Jamus ta ce a watan Afrilu za ta tura sojoji sama da 60 don gudanar da wannan aiki.

Read full article