You are here: HomeAfricaBBC2023 08 01Article 1816583

BBC Hausa of Tuesday, 1 August 2023

    

Source: BBC

Ƙasashen Yamma sun bayyana aniyar kwashe 'yan ƙasashensu daga Nijar

Tutar Nijar Tutar Nijar

Faransa da Italiya sun ce sun shirya kwashe 'yan ƙasashensu da sauran ƙasashen Turai mazauna Nijar daga ranar Talatar nan, kwana shida bayan juyin mulkin da ya kifar da ɗaya daga cikin shugabanni masu ƙawance da Ƙasashen Yamma, a cewar kamfanin dillancin labarai na AFP.

Faransa ce ta fara bayyana shirin kwashe 'yan ƙasarta daga Nijar, kafin Italiya ta sanar da irin wannan niyya, kwanaki bayan kifar da gwamnatin Bazoum Mohamed.

Matakin na zuwa ne bayan shugabannin mulkin soji a maƙwabtan ƙasashen Burkina Faso da Mali da kuma Guinea sun bayyana goyon bayansu ga sabbin mahukuntan Nijar.

Tuni dai ƙungiyar Ecowas ta yi barazanar za ta ɗauki "dukkan matakai" idan ba a mayar da Shugaba Bazoum kan karagar mulki ba.

Ita dai tsohuwar uwargijiyar Nijar wato Faransa ta ce tsaron rayukan al'ummar ƙasarta, muhimmin abu ne da take bai wa fifiko.

Faransa na da dakarun soji 1,500 a yanki, wadanda ke taimakon ƙasashen Sahel wajen yaƙi da 'yan ta-da-ƙayar-baya masu iƙirarin jihadi.

Ministar harkokin wajen Faransa, Catherine Colonna ta faɗa a ranar Litinin cewa zanga-zangar da aka yi a gaban ofishin jakadancin ƙasarta da kuma zarge-zargen cewa dakarun tsaron Faransa sun yi harbi a kan taron mutane, in ji ta duk ba gaskiya ba ne.

A cewarta abubuwan da suka faru duka al'amura ne da aka saba yi don wargaza duk wani ƙoƙari.

Juyin mulki a Nijar ya ƙara tsoron da ake da shi game da batun tsaro a yankin Sahel.

Shugabannin mulkin soji a Burkina Faso da Mali sun ce duk wnai yunƙuri na mayar da Shugaba Bazoum kan mulki da ƙarfi, za a ɗauke shi a matsayin wata shelar yaƙi.

Ana tsare da hamɓararren shugaban Nijar ɗin ne a Niamey, babban birnin ƙasar.

Read full article