BBC Hausa of Thursday, 22 June 2023
Source: BBC
Manchester City da Chelsea da kuma Liverpool dukkanninsu sun yi yunkurin sayen dan wasan tsakiya na Real Madrid, Fede Valverde, dan Uruguay a bazaran nan. (Team Talk)
Fulham na son sayen da wasan tsakiya dan Brazil, Fred, daga Manchester United. (Telegraph)
Everton za ta nemi sayen mai tsaron ragar Crystal Palace da Ingila Sam Johnstone, idan Jordan ya bar kungiyar. (Sun)
Leicester City ta yi wa dan wasanta na tsakiya dan Ingila, James Maddison farashin sama da fam miliyan 50, yayin da Tottenham da Newcastle ke nuna sha'awarsu a kansa. (Sky Sports)
Manchester City na dab da cimma yarjejeniya da matashin dan bayan RB Leipzig, Josko Gvardiol, dan Croatia mai shekara 21. (Fabrizio Romano)
Arsenal ta yi kari a taryin da ta yi wa dan wasan Chelsea Kai Havertz, na Jamus fam miliyan 60. (Mail)
Newcastle na neman kawo karshen zawarcin da take yi wa dan wasan tsakiya na Inter Milan da Italiya Nicolo Barella. (Independent)
Crystal Palace na son Roy Hodgson ya ci gaba da zama a kungiyar a matsayin kociyanta. (Guardian)
Newcastle za ta nemi sayen matashin dan wasan gaba na Jamus Derry Scherhant, mai shekara 20 daga Hertha Berlin. (Telegraph)
Arsenal ta tattauna da Southampton ko za ta sayar mata da matashin dan wasanta na tsakiya, Romeo Lavia, dan Belgium mai shekara 19. (90min)
Paris St-Germain na son sayar da tsohon dan wasan Liverpool Georginio Wijnaldum a bazaran nan. Dan wasan na Holland ya yi zaman aro ne a kakar da ta gabata a Roma. (Foot Mercato )
Fulham ta yi wa dan wasanta na tsakiya Joao Palhinha farashin fam miliyan 90, yayin da West Ham ke nuna sha'awarta a kan dan Portugal din. (Mail)
Leeds United ta kawar da batun nada kocinyan West Brom Carlos Corberan a matsayin sabon mai horad da 'yan wasanta. (Football Insider)
Tsohon kociyan Crystal Palace Patrick Vieira na daya daga cikin wadanda Leeds ke neman dauka. (Sky Sports)